More Podcasts
Duk wanda ya kai shekara 40 ko sama da haka, zai iya tuna irin tarbiyyar da ya samu daga iyayensa a baya, da kuma yadda alaƙar da ke tsakanin yara da iyaye ta ke cike da girmamawa, kulawa, da soyayya.
A yau, abubuwa sun canza sosai.
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
- NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu
Yawancin iyaye na fuskantar ƙalubale iri-iri, musamman yadda nauyin rayuwa ke ƙaruwa a kansu.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu shi ne yawaitar mata masu aiki, ko dai a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu.
Wannan sauyin yana iya shafar irin kulawar da yara ke samu daga iyayensu.
Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan ƙalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyar ’ya’yansu, da kuma irin tasirin da sauye-sauyen zamantakewa ke yi a rayuwar iyali.
Domin sauke shirin, latsa nan