Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
- Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
- Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo
Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa.
Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan, shi ma daga bisani ya rama kafin wasu su shiga tsakani.
Lamarin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ganin matar ta ci zarafin jami’in tsaron yayin da yake bakin aikinsa.