Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Barcelona da ci 3-2 a wasan hamayya da suka barje gumi a gasar Super Cup a kasar Saudiyya.
Barcelona da ta kwashi kashinta a hannun Real Madrid ne bayan da farko aka tashi kunnen doki a wasan da ya dauki hankali matuka.
Wasan ya kayatar matuka inda kungiyoyin suka murza leda gwanin ban sha’awa a gaban ’yan kallo 30,000 a filin wasa na Sarki AbdulAziz da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Real Madrid ce ta fara jefa kwallo a raga ta hannun dan wasanta Vinicius Jr., a minti na 25, sai Barcelona ta warware kwallon a minti na 41 ta hannun Luuk De Jong.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Benzema ya zura wa Real Madrid kwallo a minti 72 yayin da shi kuma Ansu Fati ya warware kwallon a minti na 83.
A haka aka tashi daga wasan, wanda hakan ya sa aka tafi karin lokaci na minti 30, don fidda gwanin da zai je zagayen karshe na gasar.
A karon farko na karin lokacin ne dan wasan tsakiyar Real Madrid, Fede Valverde ya sanya kwallo ta karshe a minti na 109, wanda hakan ya sanya kungiyar tasa lashe wasan hamayyar.
Karo na biyar ke nan a jere da Real Madrid ta doke Barcelona a dukkanin wasannin da suka gwabza.
Kazalika, Real Madrid ta je zagayen karshe na gasar ta Super Cup, inda za ta jira zakaran da ya yi nasara a wasan da za a yi a daren ranar Alhamis tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao.