Wani rahoto da Hukumar kididdiga ta kasar Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad yana dada samun gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa ’ya’yansu a yanzu.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, sunan na Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini a Ingila, yanzu ya kawar da sunan William ya hau gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara a kasar.
A alkaluman da hukumar ta fitar ta ce sunan Oliber wanda shi ne na daya a cikin sunayen da iyaye ke sanya wa ’ya’yansu maza, ya ci gaba da rike matsayinsa a yawancin sassan Ingila da yankin Wales, in ban da yankin Arewa maso Yammacin kasar inda sunan Harry har yanzu shi ne na daya. Amma a birnin Landan da yankunan Tsakiyar Yammacin kasar sunan Muhammad ne ya fi farin jini.
Rahoton ya ce a bangaren sunayen mata kuwa sunan Olibia ya maye gurbin Amelia daga matsayi na daya a Ingila da yankin Wales.
Sunan na Olibia ya sake dawowa da tagomashinsa, domin dama shi ne mafi farin jini da iyaye ke sanya wa ’ya’yansu mata a tsakanin shekarun 2008 da 2010.
Sai sunan Harper wanda ya fi samun tagomashi sosai cikin sunayen da ake rada wa ’ya’ya mata, kamar yadda Jadon shi kuma ya samu cirawa fiye da kowane suna a bangaren maza a wannan lokaci.
Sunan Harper dai shi ne Dabid Beckam da matarsa bictoria suka rada wa ’yarsu, inda a shekarar 2011 da aka haife ta aka samu jarirai mata 42 da aka sa musu sunan a Ingila da Wales.
Zuwa shekarar 2016, sunan shi ne na 44 a sunayen da aka fi sanya wa mata, wanda a lokacin an samu jarirai 1,256 da ke da sunan.
A shekarar kuma sunan mata na Lily ya kawar da Poppy daga cikin goman farko, ya maye gurbinsa.
Duk da cewa sunan Olibia ne ya fi yawa a sunayen da ake rada wa ’ya’ya mata a gaba daya, Armelia har yanzu shi ne sunan da ya fi farin jini a Yorkshire da Humber da yankunan tsakiya na gabashi da yamma da na Birtaniya da kuma Landan.
Sababbin fina-finan Star Wars ga alama sun yi tasiri kan yadda iyaye ke zabar sunayen da suke sanya wa ’ya’yansu inji rahoton.
Iyaye sun rika sa wa ’ya’yansu sunayen jaruman cikin fina-finan, ta yadda aka samu karuwar sunaye irin su Rey da Luna a mata da kuma Jadon da Arlo shi ma a maza.
Haka a lokacin da aka haifi Gimbiya Charlotte, ta hudu a jerin masu jiran gadon sarautar Ingila, sunan ya zama na 12 a jerin wadanda aka fi sanya wa jarirai mata, inda ya yi tashin gwauron zabo ya wuce mataki 13, a shekarar 2015. Shi ma dan uwanta Yarima George haihuwarsa ta sa sunansa ya samu tagomashi.
Sunansa ne na 10 a wadanda iyaye suka fi sa wa ’ya’ya maza, a shekarar 2013, wato shekarar da aka haife shi, inda shi ma ya ci gaba zuwa matsayi na bakwai a 2014, har ya kai na hudu a 2015. Kuma a shekarar 2016, ya zamo na uku, inda aka samu yara masu sunan har 5,263.
Hukumar kididdiga ta Birtaniya ba ta lissafa sunayen da aka sanya wa yara kasa da uku ba a Ingila da Wales gaba daya domin kare sirrinsu.
Hukumar ta ce, ta fitar da wannan sakamako ne bisa alkaluman da ta tattara na sunayen da ake rajistar haihuwar yara da su.