✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun yi yunkurin farke cikin kada kan ya hadiye yaro dan shekara 7

Akwai daruruwan kaddai a kogin kuma sun rika kai farmaki ga mutane.

Wadansu fusatattun mutane mazauna kauyen Raghunathpur, a yankin Madhya Pradesh Sheopur da ke kasar Indiya, sun kama wani babban kada inda suka yi yunkurin yanka shi don ceto wani yaro dan shekaru bakwai da suke zargin kadan ya hadiye shi.

Mutanen suna zargin kadan ya kai wa yaron mai suna Antar Singh farmaki ne a lokacin da yake wanka a Kogin Chambal a ranar Litinin da ta gabata kuma ya ja shi cikin kogin.

Jama’ar da abin ya faru a kan idonsu, sun kira ’yan uwan yaron wadanda suka yi gaggawar zuwa kuma suka kama kadan ta amfani da sanduna da igiya da kuma raga, suka ja shi wajen kogin.

Babban jami’in ’yan sandan yankin da jami’in kula da dazuka sun isa yankin don hana su kashe kadan, bayan da suka gamsar da su cewa a nemi yaron a cikin kogin na Chambai.

“Don haka, suka kama kadan suka daure shi tare da sa katako a tsakanin hakoransa don tabbatar da cewa baitauna yaron ba,” inji wani mazaunin.

Cike da tashin hankali ’yan uwan Antar Singh, sun ci gaba da matsa wa jami’an kula da dajin kan lallai a fede kadan don fito da yaron amma suka ki ba da kadan.

Jami’an Hukumar SDRF sun ci gaba da neman yaron a Kogin Chambal inda ayarin masu aikin ceto ya kai yamma amma bai ga alamar yaron ba. Daga nan aka dakatar da nemansa bayan duhu ya yi.

Jami’an sun sanar da mazauna kauyen cewa, idan kadan ya kama yaron, ba zai hadiye shi ba.

’Yan sanda sun ce ta yiwu yaron ya shiga wuri mai zurfi ne a kogin, kuma za a ci gaba da nemansa.

Sai dai mazauna kauyen sun ce kadan na cin mutane kuma an dauke shi tare da sakinsa a wuri mai nisa.

Kamar yadda jami’ai suka ce, akwai daruruwan kaddai a kogin kuma sun rika kai farmaki ga mutane.

Sai dai, wasu daga cikin mazauna kauyen sun yi ikirarin cewa sun ga lokacin da kadan ya hadiye yaron da ransa.