’Yan sanda sun dakile aukuwar fito-na-fito tsakanin ’yan uwan wasu iyalai biyu a jihar Taraba, bayan wani magidanci ya kashe tsohon saurayin matarsa, shi kuma jama’a suka kashe shi.
Lamarin ya auku ne a anguwar Mafindi da ke garin Jalingo, babban birnin jihar a ranar Lahadin da ta gabata.
- An gano masallacin da ya shekara 37 a cikin ruwa bai rushe ba
- LABARAN AMINIYA: Za a Dawo Buga Wasannin Gasar Firimiya ta Ingila a Ranar Talata
Binciken Aminiya ya gano cewa mijin wata mata mai suna Gaje ya sami matarsa tana magana a waya da tsohon saurayinta.
Mijin matar, mai suna Abdulrashid Adamu a cewar wani ganau, ya kwace wayar daga hannunta domin gano wanda take wayar da shi, inda ya gano cewa tsohon saurayinta ne wanda ya kasa kafin ya aure ta.
Majiyar ta shaida wa Aminiya cewa mijin ya yi kamar ya manta da lamarin, amma kashegari bayan sallar Isha’i sai ya tafi hanyar da tsohon saurayin matarsa tasa ke bi ya labe dauke da wuka.
Jim kadan sai ga tsohon saurayin matarsa mai suna Dahiru zai tafi gida, inda Abdulrashid din ya yi masa magana suka gaisa, sai kawai ya daba masa wuka a wuya.
Bayan aikata hakan ne sai ya sulale ya koma gida.
Da isarsa sai ita matar tasa ta lura mijin hankalinsa ya tashi, da ta tambaye shi me yake faruwa sai ya ce mata ba komai.
Majiyar ta kuma shaida wa Aminiya cewa matar ta ga jini a rigar mijin nata kuma dama ya sha yin barazanar kashe tsohon saurayin matar tasa.
Sai dai a cikin daren labari ya cika unguwar cewa an kashe Dahiru, kuma wanda aka fara zargin shi ne Abdulrashid, saboda wasu daga cikin jama’ar anguwar sun gan shi a labe cikin duhu a hanyar da tsohon saurayin matarsa tasa yake bi.
A cikin binciken da yan sanda suka gudanar kan wannan kisan, sun ce sun kama mata inda ta shaida wa musu a gaban manyan unguwa cewa mijinta ne ya kashe tsohon saurayin nata saboda ya sha yin barazanar haka a baya.
Daga nan ne aka saki matar aka kama mijin nata, inda matasa da wasu zauna-gari-banza suka kwace shi daga hannun ’yan sanda suka kashe shi suka kuma yar da gawarsa a kan hanya.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.