Tauraron fina-finan Hollywood na Amurka, Steven Seagal, ya lashi takobin tsayawa kai da fata wajen goyon bayan Rasha.
Fitaccen jarumin ya kai ziyara zuwa birnin Mosko na kasar Rasha, inda ya halarci wani kasaitaccen liyafa da aka shirya domin bikin cikar shugaban kasar, Vladimir Putin shekara 70 a duniya.
- Yadda ruwan saman farko ‘ya yi gyara’ a Maiduguri
- Yadda matasa 29 suka rasu a nutsewar jirgin ruwa a Sakkwato
A wani bidiyo da ya yi a wurin kasaitaccen liyafar Steven Seagal, wanda aka gani a tsakiyar wasu mayan ’yan bokon Rasha da kasashen Yamma suka sanya wa takunkumi kan mamayar da kasarsu ta yi wa Ukraine, jarumin na Hollywood ya jaddada goyon bayansa ga mukarraban Putin, duk da takunkumin da Amurka da kasashen Turai suka kakaba wa Rasha.
Mahalarta liyafar sun hada da Babban Editan gidan talabijin na RT na Rasha, Margarita Simonyan, da mai gabatar da shirye-shirye talabaijin na gwamantin kasar, Vladimir Soloviev, wanda ya fito ya goyi bayan mamayar da Putin ya kadamar a Ukarine.
Daga Vladimir Soloviev, wanda ya zargi Birtaniya da zuzuta zargin kisan fararen hula a yankin Bucha, yana daga cikin mutanen da ke tsaye a kusa da Steven Seagal.
Margarita Simonyan da Vladimir Soloviev suna daga cikin mutanen da kasashen Turai suka kakaba wa takunkumi kan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.
Jaridar Financial Times ta Amurka ta ce Seagal ya gabatar da jawabin nasa ne a ranar 10 ga Afrilu , 2022.
Addressing the audience, Seagal said, “Kowannenku iyalai da aminaina ne, ina kaunar ku kuma zan kasance da ku, duk rintsi.”
Seagal, wanda na hannun daman Shugaba Putin ne na iya jefa kansa cikin tsaka-mai-wuya, ganin yadda kasashen Yamma suka yi taron dangi wajen la’antar mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.
‘Seagal dan Rasha’
A shekarar 2016 Rasha ta ba wa Seagal takardar fasfon kasarta, sannan a 2018 ta nada shi a matsayin manzonta na musamman a Amurka.
A lokuta da dama an ga Putin tare da Steven Seagal, wanda a baya ya bayyana Putin din a matsayin “daya daga cikin manyan shugabannin duniya da ke rayu.”
A wata hira da aka yi da shi a watan Fabrairun da aka fara yakin, ya yi zargin cewa ’yan waje ne ke neman gwara kan Rasha da Ukraine su yaki juna.
An dade dai ana caccakar Rasha kan mamayar da ta kaddamar a Ukraine.