✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sterling Bank ya bullo da tsarin wutar lantarki mai nagarta

Bankin kasuwanci na Sterling Banki ya kaddamar da sabon tsarin samar da wutar lantarki mai amfanin da hasken rana, mai sauki ga gidaje da kamfanoni…

Bankin kasuwanci na Sterling Banki ya kaddamar da sabon tsarin samar da wutar lantarki mai amfanin da hasken rana, mai sauki ga gidaje da kamfanoni mai suna AltPower.

Tsarin wutar lantarkin na Altpower wanda sashen bayar da rance mara ruwa na bankin (SAF) ya kaddamar na da sauki da kuma ya samar da zabi gwargwadon halin masu bukata.

Shugaban Sashen Kasuwancin Zamani na SAF, Mohammed Yunusa ya ce, “Altpower zai samar da wutar lantar mai sauki da nagarta ga gidaje da masu sana’o’i da ba sa samun wutar lantarki sosai da kuma mazauna da masu kasuwanci a yankunan da babu wutar gaba daya”.

Shugaban Sashen Kasuwancin Zamani na SAF, Mohammed Yunusa a cikin wata sanarwa, ya ce, “Yana da inganci da sauki kuma an tsara shi da sauki ta yadda kowa zai iya samun biyan bukatarsa ta wutar lantarki”.

Masu bukata na iya samun na’uarar AltPower ta hanyar saye a lokaci guda ko kuma a hankali. Ya ce wadanda ba za su iya saye a lokaci guda ba na da damar biyan kudin cikin shekara guda ba tare da an dora musu kudin ruwa ba.

Bayan haka mutane na kuma iya shiga tsarin amfani da wutar ta yadda za a rika cazar su daidai abin da suka sha (PAAS) a wata-wata.

Za a ba wa masu shan wutar ta tsarin PAAS na’urar amfani da hasken rana kyauta ba tare da sun biya kudin hadawa ko kafin alkalami ba, amma za su biya kudin haya a duk wata.

Inusa ya ce amfanin AltPower sun hada da magance kudaden da ake kashewa na sayen man janareto da karar da ke damun su, sannan ya samar da wutar lantarki mai inganci.