✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Stephen Keshi bai ajiye aiki ba -Hukumar NFF

A shekaranjiya Laraba Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF)  ta karyata labarin da ake bazawa cewa kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles…

A shekaranjiya Laraba Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF)  ta karyata labarin da ake bazawa cewa kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya yi murabus.
Jim kadan bayan kasar Faransa ta doke Najeriya da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya a Brazil a ranar Litinin da ta wuce ne aka yayata labarin cewa Keshi ya ajiye mukaminsa.
Kafin nan, an samu labarin wasu daga cikin ’yan kwallon da suka hada da Joseph Yobo sun bayyana cewa sun yi ban kwana da kungiyar da hakan ta sa wasu suka kara da cewa shi ma Keshi yana daga cikin wadanda suka yi murabus din.
Mai magana da yawun hukumar NFF ne ya karyata wannan batu.  Ya kara da cewa kodayake Keshi ya fada wa manema labarai bayan an tashi wasan cewa  lokaci ya yi da zai fuskanci iyalinsa hakan ce ta sa wasu suka dauka ya ajiye aiki da hukumar ne.
“Ya zuwa wannan lokaci ba mu karbi takardar barin aiki daga wajen Keshi ba, don haka labarin da ake bazawa ya zama na kanzon-kurege”, inji shi.
Hukumar ta ce sakon ajiye aiki da wasu suka ce sun gani a kafar sadarwar Twitter ta Keshi ba gaskiya ba ne don an gano Keshi ba ya amfani da kafar sadarwar Twitter ballantana har ya aiki sako ta kafar.