Hukumar tsaron Farin Kaya (SSS) a Jihar Kano ta kama wani mawaki mai suna, Ahmad Abdul, kan wata wakar batanci ga Addinin Musulunci da ya fitar.
Hukumar ta ce ta ajiye mawakin a wani wurin tsare jama’a mai cike da tsaro domin gudun kada al’ummar gari su afka masa, musamman ganin yadda ta yamutsa hazo a Jihar.
Sai dai bayanai sun ce, mawaki Abdul, ya nuna nadama tare da neman gafarar daukacin al’ummar Musulmi da Gwamnatin Jihar Kano da ma malaman addinin Musulunci.
Ya shaida wa hukumar ta SSS cewa bai san wakar ta saba da koyarwar Musulunci ba.
Da yake tsokaci a kan lamarin, Babban Sakataren Hukumar Tace Finai-finai ta Kano, Ismaila Afakallah, ya ce ya samu daruruwan sakonnin korafi daga jama’ar gari a kan wakar.
Malam Afakallah ya ce ya kai rahoton mawakin ga hukumar ta SSS, inda jami’anta suka kama shi a wani otel din da yake boye tsawon lokaci.
Mahaifin mawakin, mai suna Abdullahi Isa, ya ce ya gode wa hukumar ta SSS kan yadda ta yi hanzarin kawo dauki da ya hana rincabewar lamarin, inda jama’a za su dauki doka a hannunsu.
Ko a watan Agustan bara sai da wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zama a unguwar Hausawa Filin Hockey a birnin Kano, ta samu wani matashin mawaki mai suna, Yahaya Sharif-Aminu, da laifin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) inda ta yanke masa hukuncin kisa, kan yada wakar da ya yi a kafar WhatsApp.
Sai dai daga bisani, sashen daukaka kara na babbar Kotun Jihar Kano a ranar 21 ga watan Janairun 2021 ya soke hukuncin kisan.