Ƙasar Spain ta samu tikitin zuwa wasan ƙarshe na gasar Euro da ake bugawa a ƙasar Jamus, bayan doke Faransa da ci 2 da 1.
Ɗan wasan gaban Faransa, Kolo Muani ne ya fara jefa mata ƙwallo a minti na 8 da fara wasa.
- Yadda aka yi arangama tsakanin ’yan daba da matasa a masarautar Rano
- An ɗaure malami shekara 20 kan sukar gwamnati a Saudiyya
Spain ta warware ƙwallon a minti na 21 daga hannun matashin yaron nan, Lamine Yamal a minti na 21.
A minti na 25 ne da Dani Olmo ya ƙara wa Spain ƙwallo ta biyu.
Idan ba a manta ba Spain ce ta doke masu masaukin baƙi a wasan kwata final da ci 2 da 1, wanda ya ba ta damar zuwa matakin kusa da na ƙarshe.
Yanzu Spain za ta yi dakon wanda ya yi nasara a tsakanin ƙasar Ingila ko Netherlands a wasan da za su fafata a ranar Laraba da misalin ƙarfe 8 na dare.