Southampton ta tankado keyar Manchester City daga Kofin EFL wata Carabao bayan doke ta da ci 2-0 a ranar Laraba.
Wannan dai ita ce nasara mafi girma da kociyan Southampton Nathan Jones ya yi a dan takaitaccen aikinsa, inda ya kai kungiyar wasan kusa da karshe na cin Kofin na Carabao.
Sai dai Hausawa na cewa idan bera da sata to ita ma daddawa da wari, domin kuwa Kociyan Manchester City Pep Guardiola bai fito kwansa da kwarkwata ba yayin da ya ajiye manyan ‘yan wasansa, irin su Erling Haaland da Kevin de Bruyne.
Masu sharhi kan al’amuran wasanni na hasashen ya yi hakan ne saboda tsimin manyan ’yan wasan a dalilin karawar hamayya da za su yi a karshen makon nan da Manchester United a Old Trafford.
Tun a kashin farko na wasan ne aka yi ta kare jini biri jini, inda Sekou Mara ya fara daga ragar Manchester City bayan minti 23 da take leda, sai kuma kwallo ta biyu wadda bayan minti biyar da ta farko, Moussa Djenepo ya faki golan City Stefan Ortega ya fito, kuma ya dankaro masa kwallo daga can nesa, ta kwana a raga.
Ganin wankin hula zai kai shi dare, kociyan City, Guardiola nan da nan bayan hutun rabin lokaci ya sako De Bruyne da Haaland, to amma ya makaro, domin Southampton sun tashi haikan suka tsare bayansu da niyyar lalle sai sun kai wasan kusa da karshe, inda za su hadu da Newcastle.
Manchester City sun je wasan ne a matsayin wadanda ake ganin za su yi nasara a karawar su kai wasan kusa da karshe, a kan Saints din wadanda ke fama a gasar Firimiyar Ingila, to amma sai labari ya sha bamban, inda Zakarun na Firimiyar suka girbi abin da suka shuka na rashin tabuka abin-a-zo-a-gani.
Duk da cewa Guardiola ya yi sauyi a jerin ‘yan wasansa to amma duk da haka akwai kwararru irin su Kyle Walker da Aymeric Laporte da Jack Grealish da Ilkay Gundogan da Joao Cancelo da Phil Foden da kuma Julian Alvarez da ya dauki Kofin Duniya da Argentina.
Duk da cewa Kofin na Carabao ba lalle ba ne ya damu Guardiola ko City sosai to amma dai rashin nasarar abu ne da zai bata wa kociyan da kungiyar rai matuka.