Mahukunta kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun yanke hukuncin barin kocinsu, Solskjaer, ya ci gaba da jan ragamar kungiyar bayan shan kashi a hannun Liverpool.
Mahukuntan sun amince tare da barin kocin, inda zai jagoranci kungiyar a wasan da za ta kara da Tottenham a ranar Asabar mai zuwa.
- Iyaye sun fara sayar da ’ya’yansu don sayen abinci a Afghanistan
- Fusatattun mutane sun kashe masu ba ’yan bindiga bayanai a Kaduna
Tsohon kocin kungiyar, Sir Alex Ferguson ya nuna goyon bayansa ga Solskjaer duk kuwa da matsin lambar da yake fuskanta.
Sai dai an ba wa kocin dama a wasannin Manchester United da za ta kara da Tottenham da Atalanta da kuma Manchester City.
Tuni aka fara alakanta Antonio Conte da Zinedine Zidane da karbar aikin horas da kungiyar.
Manchester United ta shiga tsaka mai wuya a baya-bayan nan, inda ta yi rashin nasara a wasanni biyu a jere a gasar Firimiya, amma wasanta da Liverpool ya fi barin baya da kura.