Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar Jigawa ta yi kurarin kaurace wa babban taron uwar kungiyar muddin ba a yi mi’ara koma baya kan soke gayyatar Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ba.
Shugaban reshen, Garba Abubakar a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ya ce reshen na adawa da matakin da uwar kungiyar na janye gayyatar da ta yi wa gwamnan a matsayin mai jawabi ba.
A ranar Alhamis ne dai Kwamitin Zartarwar NBA ya bayar da kai bori ya hau bayan wasu ‘yan kungiyar sun yi barazanar kaurace wa taron idan har El-Rufai zai yi jawabi a taron na shekara-shekara.
Sakamakon haka kungiyar ta janye gayyatar bisa hujjar korafin ‘ya’yan nata da suka nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnana ke tafiyar da al’amuran tsaro a yankin Kudancin Jihar Kaduna ba.
To sai dai reshen NBA na Jigawa ya ce, “Zarge-zargen ba su da tushe ballantana wata alaka da kungiyar.
– Ba a yi masa adalci ba; Mu ma mun san doka
“Babban abin takaicin shi ne yadda ba a ba gwamnan damar kare kansa daga zarge-zargen da bangaren kungiyar ya yi masa kafin a kai ga cimma matsayar ba, domin kungiyar ta kowa da kowa ce”, inji shi.
Ya kara da cewa a matsayin kungiyar mai taken ‘Tabbatar da doka’ dole ta yi adalci, wanda ke nufin sai ta ba gwamnan damar kare kansa kafin ta dauki mataki.
“Idan da abin da mutane suke fada ake dogara wajen daukar mataki ba tare da bin diddigi ba, to kamata ya yi a ce an dauki makamancin wannan matakin a kan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda shi ma aka samu kwararan zarge-zarge a kansa, ciki har da na rusa gidaje da wuraren ibada ba bisa ka’aida ba.
“Saboda haka ba zai yiwu a ce wani bangare na kasa ya rika kokarin raba kanmu ba, tunda dai mun san doka.
“A kan haka muke kira ga uwar kungiya karkashin jagorancin Usoro, SAN, ta janye matakin cikin gaggawa, ko kuma reshenmu na Jihar Jigawa ba zai halarci taron na kasa da ke tafe ba”, inji Abubakar.
– Dakatarwar da El-Rufai ya yi daidai, inji IMN
Wannan tataburzar na zuwa ne bayan wata kungiyar mabiya akidar Shi’a ta IMN ta duna yoyon bayanta da matakin kungiyar na soke gayyatar da ta yi wa gwamna.
IMN ta ce bai dace gwamnan ya zama mai jawabi a taron masu ksare doka da adalci ba, alhali a cewarta ya yi kaurin suna wurin karya doka da tauye hakkin dan Adama.
– El- Rufai ya yi wa NBA kakkausan suka
Ko kafin nan El-Rufai ya ce ba abun da ya dada shi da kasa saboda janye gayyatar.
Ya ce hasali ma kungiyar ce da kanta ta nemi ya zo ya zama daga cikin masu jawabi a taron.
Gwamnan ya ce batun zama dan kasa na gari al’amri ne da ya kamata a ci gaba da tattaunawa a kai, ba sai a taron NBA kawai ba; kuma ba zai zai daina gaskiya kamar yadda ya saba ba.