✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Sudan sun katse intanet gabanin zanga-zanga kan adawa da mulkinsu

’Yan gwagwarmayar Sudan dai na amfani da intanet wajen shirya zanga-zanga.

Hukumomin kasar Sudan sun katse hanyoyin sadarwa da na intanet, tare da jibge dakaru a birnin Khartoum gabanin sabuwar zanga-zangar da aka shirya gudanarwa kan adawa da mulkin sojoji a kasar.

A Sudan dai, ’yan gwagwarmaya na amfani da intanet wajen shirya zanga-zanga da kuma watsa ta kai tsaye ta kafofin sadarwa.

Dimbin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an sun rika sintiri a a babban birnin kasar ranar Alhamis, yayin da aka yi amfani da kwantainoni wajen rufe gadar kogin Nile, wacce ta hada yankin Arewacin kasar da birnin Omdurman.

Kazalika, an ga wani shinge na wasu motocin silke wanda aka girke a daya daga cikin gadojin da aka bari ba a rufe ba.

Zanga-zangar dai da aka shirya gudanarwa ita za ta zama ta 11 tun juyin mulkin da aka yi ranar 25 ga watan Oktoba, wanda ya kai ga hambarar da Abdallah Hamdok daga matsayin Firaiminsita, kafin daga bisani a dawo da shi.

Masu zanga-zangar dai da ke adawa da mulkin sojojin kasar sun dangana har kusa da Fadar Shugaban Kasar, duk da fesa barkonon tsohuwar da aka yi a kansu da kuma katse hanyoyin sadarwa.

Wani kwamitin likitocin kasar dai ya ce sama da mutum 200 suka jikkata yayin zanga-zangar, ciki har da wanda aka harba da harsasan roba.

Akalla mutum 48 ne jami’an tsaro suka kashe tun lokacin da aka fara zanga-zangar a titunan kasar.

Wata majiya daga wani kamfanin sadarwa na kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa umarnin rufe intanet din ya fito ne daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasar

%d bloggers like this: