✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Saudiyya sun dakile harin mayakan Houthi

Dakarun Rundunar da kasar Saudiyya ke jagoranta wurin yaki da ’yan tawayen Houthi sun dakile harin kungiyar a ranar Juma’a. Dakarun ahdin gwiwar sun ce…

Dakarun Rundunar da kasar Saudiyya ke jagoranta wurin yaki da ’yan tawayen Houthi sun dakile harin kungiyar a ranar Juma’a.

Dakarun ahdin gwiwar sun ce sun tarwatsa wani jirgin ruwa makare da ababen fashewa a kan Tekun Bahar Maliya.

Gidan Talabijin na kasar Saudiyya, Ekhbariya ya ce dakarun sun kuma tarwatsa wasu jiragen yaki marasa matuka na ’yan Houthi da suka yi yunkurin kai hari a Saudiyya.

Tun shekarar 2015 Rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagorantar yaki da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan ’yan tawayen na Houthi.

’Yan Houthi na ta kai hare-haren rokoki a kan yankunan kasar Saudiyya daga kasar Yemen.

Kasar Yemen ta jima tana fama da rikin ’yan Houthi da ke yakar gwamantin kasar wadda ke da goyon bayan Saudiyya.