A matsayin wani mataki na kokarin ganin bayan ’yan ta’adda a Najeriya, Rundunar Sojin Sama ta kasar ta kaddamar da wata rundunar tsaro ta musamman mai suna ‘Operation Babu Tausayi’.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rundunar, Shugaban Sojojin Sama na Najeriya, Iya Mashal Oladayo Amao, ya bukaci shugabannin rundunar su nuna ba sani ba sabo tare da amfani da karfin makamai a kan ’yan ta’addan da suka addabi kasar nan.
- Kwastam ta kama kayayyakin fasa-kwauri na N232m a Adamawa da Taraba
- IPOB ta kashe ’yan Arewa 7 a Imo
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Laraba ta ce, Amao ya yi wadannan bayanan ne yayin kaddamar da rundunar ranar Talata a Kaduna.
A cewar Amao, nuna rashin tausayi a kan ’yan ta’addan zai taimaka wajen hana su walwala da damar zirga-zirga, tare da saka kwarin gwiwa ga ’yan kasa dangane da yaki da ta’addancin da ake yi.
Babban hafsan ya ce babu tabbas kan zirga-zirgar ‘yan taddan tsakanin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.
Don haka ya ce akwai bukatar rundunar ta rika sauya salonta domin ta daidaita da kowane yanayi a fagen yaki da ’yan ta’addan.
‘“Muna dauke da hakkin kare kasarmu da kuma bai wa ‘yan kasa kwarin gwiwa. Don haka ya zama wajibi mu zama a shirye a kowane lokaci don tunkarar makiya.
“Don haka, na kalubalance ku kada ku nuna sassauci kan kowane dan ta’adda da masu taimaka musu, kana ku hana su damar zirga-zirga da tada wa ’yan Najeriya hankali,” inji Amao.
Daga nan, ya bai wa dakarun tabbacin ci gaba da samar musu da kayan aiki masu inganci da kuma magance kalubalen da suke fuskanta.