Sojojin kasar Isra’ila a karon farko sun da cewa dakarunsu sun kutsa kai cikin Zirin Gaza domin kai harin kan kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, sojojin sun ce sun shiga Gazan ne domin su yaki ’yan Hamas, su lalata makamai sannan su nemo Yahudawan da aka kama aka boye.
Sai dai sanarwar na nuna cewar akwai alamun ci gaba da dauki-ba-dadi a nan gaba kadan.
Tun bayan harin da Hamas ta kaddamar a kan Isra’ila a ranar Asabar din da ta gabata kasar take ta tarawa tare da girke jami’an tsaro domin ta far wa Falasdinawan.
Idan za a iya tunawa, Isra’ila ta bayar da umarnin kwashe dukkan fararen hular da suke a birnin Gaza da kuma Arewacin Zirin saboda za ta fara ruwan wuta a kan Falasdinawa.
Umarnin na zuwa ne ranar Juma’a, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya take cewa Isra’ila ta gargade ta da ta kwashe mutum miliyan 1.1 da suke Zirin na Gaza nan da awa 24.
Hakan na zuwa ne yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin kungiyar Hamas ta Falasdinawa da Isra’ila ya shiga rana ta bakwai.
Sojojin Isra’ila dai sun yi zargin cewa dakarun Hamas na buya a cikin fararen hula a birnin na Gaza.
A wata sanarwa da sojojin na Isra’ila suka ba fararen hula, sun ce, “Saboda amfaninku muke bayar da wannan shawarar.
“Za ku sami damar sake komawa Gaza ne kawai lokacin da muka bayar da umarnin yin hakan. Kada ku kuskura ku tsallaka shingen da Isra’ila ta kafa,” in ji sanarwar.
Sojojin sun kuma ce a ’yan kwanaki masu zuwa za su ci gaba da ruwan wuta a yankin, amma sun ce za su iya bakin kokari wajen ganin hakan bai shafi fararen hula ba.
Sama da mutum 1,500 ne dai kasar Isra’ila ta kashe tun bayan fara rikicin a Zirin Gaza, galibinsu mata da kananan yara.
Sai dai tuni kungiyar Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila inda ta kira shi da farfagandar karya.