Hukumoni a Zirin Gaza sun ce Falasdinawa 240 Isra’ila a kashe, ta kuma jikkata wasu 650 daga ranar Juma’a.
Hukumar Hamas ta ce Isra’ila ta kai hare-hare sama da 400 da jirage da kuma ta kasa a sassan Gaza tun bayan karewar wa’adin tsagaita wuta da bangarorin suka yi.
Hamas ta ce sojojin Isra’aila sun tsananta hare-hare a sassan yankin Khan Younis da ke Kudancin Zirin Gaza inda suka rika rusa gidaje da mutane a cikinsu.
Tun bayan karewar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutan mako guda da Hamas da Isra’ila suka cim-ma, sojojin Isra’ila suka rika ragargazar yankunan Gaza.
Akasarin wadanda hare-haren Isra’ila yi ajalinsu a Gaza dai kananan yara ne da tsofaffi da kuma mata.
A kimanin wata biyu da Isra’ila ke ragargazar Gaza, yawan Falasdinawan da ta kashe sun haura mutum dubu 15.