✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda hakimai 3 suka mutu a hatsarin mota a Oyo

Wasu manyan hakimai uku sun rasua hadarin mota a yankin Arinkinkin da ke Jihar Oyo.

Al’ummar Masarautar Ogbomoso a Jihar Oyo sun kidime da juyayi da rasuwar manyan hakimai uku a hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Arinkinkin da ke Karamar Hukumar Orire.

Hakiman da suka rasu a ranar Juma’a sun hada da Olodogbo na Odogbo da Onibowula na Bowula da kuma Alayetoro na Ayetoro.

Wata majiya mai tushe ta ce, sarakunan da suke cikin mota daya suna kan hanyar zuwa jana’izar dan uwan wani takwaransu wato Oloolo na Oolo Oba Oyebunmi Ajayi ne a lokacin da hadarin ya auku.

Majiyar ta bayyana cewa, motar da suke ciki ce ta yi karo ne da wata babbar mota inda nan take suka rasa rayukansu.

Mutum na hudu da ke cikin motar, wanda ake kyautata zaton direban motar ne ya samu raunuka da yanzu haka likitoci suke kokarin ceton ransa.

An kai gawarwarkin Asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomoso.