Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutum 16, yayin da wasu hudu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Kano zuwa Kaduna.
Kwamandan hukumar a jihar, Kabir Nadabo ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a Kaduna.
A cewarsa, hatsarin ya auku ne a ranar Lahadi, a mahadar Taban Sani kusa da Tashar Yari da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna.
Nadabo ya ce, “Hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota bas mai lamba TRB 674ZG, wadda ta taso daga Jihar Kano zuwa Jihar Benuwe.
“Mun aike da tawagar jami’anmu na Tashar Yari, inda suka kai dauki wajen da hatsarin ya auku.”
Ya ce binciken da aka gudanar, ya nuna cewar mutum 20 ne hatsarin ya rutsa da su, mutum 16 sun rasu sannan wasu hudu sun jikkata.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin kula da su , yayin da aka kai gawar wadanda suka rasu zuwa Asibitin Koyarwa na ABU da ke Shika a Zariya.
Kwamandan hukumar, ya shawarci masu ababen hawa da su guji gudun wuce kima.
Ya ce hakan zai taimaka wajen tsira da rayuka ko dukiyoyin jama’a a duk lokacin da aka samu hatsari.
Kwamandan, ya ce FRSC na ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran kungiyoyin sufuri wajen wayar da kan direbobinsu kan ka’idojin tuki, domin kaucewa hatsari.