✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota a Neja

Jumullar mutane 13 ne suka rasa rayukansu a hatsarin motar da suka hada da sirikin amaryar

Wata sabuwar amarya da kawayenta biyar sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kusa da Lukoro da ke garin Edati a jihar Neja ta Najeriya a ranar Juma’ar da ta gabata.

Jumullar mutane 13 ne suka rasa rayukansu a hatsarin motar da suka hada da sirikin amaryar da wasu karin mutane 6 kamar yadda Hukumar Kiyaye Haddura ta Najeriya ta bayyana, tana mai danganta hatsarin da gudun wuce sa’a.

Bayanai na cewa, motocin da suka yi taho-mu-gaman sun hada da kirar Toyota Corolla wadda ta taso daga Mokwa zuwa Bidda da kuma motar bas ta ‘yan kasuwa kirar Nisan da ke kan hanyarta ta zuwa Minna, babban birnin jihar Niger zuwa Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Najeriya, reshen jihar Niger, Tsukwan Kumar, ya ce, an samu asarar rayukan mata takwas da kuma maza hudu, sai kuma wani karamin yaro guda.

Tuni aka mika gawarwakin mutane 9 ga iyalansu, yayin da sauran mamatan aka garzaya da su dakin ajiyar gawarwaki da ke babban asibitin koyarwa na Kutigi kamar yadda Mista Kumar ya bayyana.

Ana yawan samun asarar rayukan al’ummar  Najeriya a hadduran motoci da masana ke dangantawa da musabbabai daban-daban da suka hada da tsananin gudu da lalacewar hanya da tukin ganganci da rashin hakuri da dai sauransu.