Sojojin Isra’ila sun ƙara kai wasu ƙarin hare-hare a Rafah da ke kudancin Gaza ta hanyar amfani da tankokin yaƙi da makaman atilare a safiyar wannan Asabar.
Isra’ila na ci gaba da kai karin hare-hare a yankin Rafah da ke Zirin Gaza, duk da irin kiraye-kirayen da ƙasashen Yammaci ke yi mata domin dakatar da ɓarin wutar da ta ke yi a wasu muhimman sassa na Falasɗinu.
- Obaseki ya cika alƙawarin ƙarin albashi a Edo
- Me zai faru tsakanin Dortmund da Madrid a wasan karshe na Zakarun Turai?
Ana iya tuna cewa, a baya bayan nan ne Kotun Manyan Laifuka ta Duniya ICJ ta umarci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a yankunan da ta saba amma ta yi kunnen ƙashi.
Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 239, wadda ya kashe aƙalla Falasɗinawa dubu 36,284 kuma kashi 71 daga cikinsu mata ne da kananan yara da jarirai.
Haka kuma, hare-haren ya jikkata mutum 82,057 a cewar hukumomi, yayin da fiye da mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine.
Wannan ruwan wuta da Isra’ilar ke yi na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa Isra’ila ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare na tsagaita wuta ta dindindin.
Jim kaɗan bayan Biden ya bayar da sanarwar, sai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙin da take yi har sai ta cimma muradunta, daga ciki har da gamawa da Hamas.
Sai dai a nata ɓangaren, ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa a shirye take domin ta yi aiki da tsare-tsaren da ake da su a ƙasa na tsagaita wutar.