Dakarun Sojin haɗin gwiwa da ke aiki ƙarƙashin Operation Lake Sanity 2, sun yi nasarar ceto mata da ƙananan yara 34 daga hannun Boko Haram a ƙauyen Wulgo na ƙaramar hukumar Ngala a Jihar Borno.
Mai Magana da yawun dakarun haɗin gwiwar, Laftanal Kanal Abdullahi Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin.
- Hawan Daushe: Yadda Sarkin Zazzau ya karɓi gaisuwar sallah
- Sarautar Kano: Babu barazanar da wani zai yi mana —Kwankwaso
Ya bayyana cewa baya ga kuɓutar da mutanen da aka sace, dakarun sun kuma yi nasarar hallaka ɗan ta’adda a yayin samamen.
A cewarsa samamen ya gudana ne ranar 15 ga watan Yuni, a ƙauyukan Mazuri da Itsari da Mudu da kuma Maleri dukkaninsu a iyakar Najeriya da Kudancin yankin tafkin Chadi.
Kazalika, ya ce wasu mayaƙan ISWAP uku da ke zaune a sansanin Jabilaran, sun miƙa wuya yayin samamen a ranar Litinin.
Mayaƙan sun haɗar da Babakura Abubakar mai shekara 20 da Abacha Kyari mai shekara 28 sai Mohammad Adam mai shakara 29, waɗanda yanzu ke hannun dakarun don gudanar bincike.