Dakarun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya sun yi wa sansanonin ’yan ta’adda ruwan wuta a dajin Tumbun da ke gabar Tafkin Chadi a Jihar Borno.
Sojojin kamar yadda wakilinmu ya ruwaito sun yi raga-raga da sansanonin ’yan ta’addan wanda ke dauke da gine-ginensu na daukan horo da atisaye.
- An gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison-Madueke a Birtaniya
- Kotu ta soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Air Commodore Edward Gabkwe, Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Rundunar Sojin Saman Najeriya ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun cikin jiragen yaki kirar Tucano sun kai farmakin ne a yankunan Tumbun Fulani da Tumbun Shitu a tsakanin ranakun 27 zuwa 30 ga watan Satumban 2023.
Wakilinmu ya ruwaito cewa sojojin sun kai farmakin ne bayan samun tabbacin cewa ’yan ta’adda na gudanar da wasu ayyuka a wuraren da ke zama barazana ga ayyukan soja da sauran mazauna yankin.
Bayanai sun ce an hango ’yan ta’adda a yankin na Tumbun Fulani suna loda jarkoki a cikin motoci 2 da aka boye a karkashin bishiyoyi.
Wannan ce ta sanya sojojin suka kai samame yankin da ake zargin maboyar makamai ce ga ’yan ta’addan na Boko Haram da ISWAP.
Bayan wadannan hare-hare na dakarun sojan saman binciken ya nuna cewa an kashe ’yan ta’adda da dama tare da lalata manyan bindigogin yaki.
Kazalika, sojojin sun kai irin wannan harin a Tumbun Shitu bayan an samu wasu gine-ginen da ake kyautata zaton maboyar ‘yan ta’adda ce.
A yayin bincike an samu motoci 3 dauke da manyan bindigogin harbo jiragen sama tare da dimbin ’yan ta’adda da ke shige da fice a wurin.
A baya bayan nan dai rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da fadi-tashin takaita ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da ma sauran sassan Najeriya.
Alkalumma sun nuna cewa ana samun hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro wanda bayanai sun tabbatar da cewa hakan na tasiri wajen samun ire-iren wadannan nasarori a kan ’yan ta’adda.