✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa

Bayanai sun ce biyu daga cikin alkalan uku ne suka soke nasarar Gwamna Abdullahi.

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a birnin Lafia ta soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa.

Kotun wadda alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Ezekiel Ajayi suka yanke hukunci, ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa INEC da ta janye shaidar lashe zabe da ta bai wa Gwamnan.

Bayanai sun ce biyu daga cikin alkalan uku ne suka soke nasarar Gwamna Abdullahi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, kotun ta kuma ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Ana iya tuna cewa, a sakamakon da INEC, ta ce Gwamna Sule na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 347,209 yayin da abokin takararsa, Mista  Ombugadu ya samu kuri’u 283,016.