Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta rarraba wa ɗalibai marasa galihu littafan rubutu a Jihar Nasarawa.
Sanata Tinubu wadda ta bayyana samar da nagartaccen ilimi a matakin farko a matsayin tubalin ci gaban ƙasa, ta yi rabon littafan rubutun ne guda 60,000 ga ɗalibai marasa galihu a faɗin ƙananan hukumomi 13 na Jihar Nasawara.
- INEC ta soma tattara sakamakon Zaɓen Gwamnan Edo
- Zaɓen Edo: Abin da ya kai ni Ofishin INEC — Obaseki
Da take ƙaddamar da rabon littafan, uwargidan shugaban ƙasar wadda matar Gwamnan Nasarawa, Salifat Abdullahi Sule ta wakilta, ta ce ilimi a matakin farko wani bigire ne da ke da muhimmanci wajen bunƙasar Nijeriya.
Yayin da take bayyana lamarin a matsayin wani ɓangare na Shirin Sabunta Fata, Remi Tinubu ta jaddada ƙudirin Gwamnatin Nijeriya a dukkan matakai wajen bunƙasa harkokin ilimi ta fuskar inganci da kuma sauƙi musamman a tsakanin waɗanda ke da rauni a cikin al’umma.
Ta buƙaci mahukuntan makarantun da suka samu tallafin littafan da su tabbatar ɗaliban sun ci moriya yadda ya kamata.
Uwargidan Shugaba Ƙasar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana sayar da littafan rubutun zai kuka da kansa.
A nasu jawaban, Kwamishinan Ilimi na Jihar Nasawara, Dokta John Maman da Shugabar Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko (SUBEB), Hasiya Ahmed, sun jinjina wa wannan Shirin na Sabunta Fata da cewar ya zo a daidai kan gaɓar da ake buƙatar tallafi a yankunan karkara musamman a wannan lokaci da akw fuskantar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar
Sauran mahalarta sun haɗa da Kwamishinar Harkokin Mata da Bunƙasa Al’umma da Kwamishinan Ilimi na Musamman a Jihar Nasawara.