Dakarun sojin Najeriya sun yi raga-gara da mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP a Gandun Namun Dajin Kainji da ke Jihar Neja.
Mayakan kungiyar ta ISWAP sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin ne a yayin da suke kokarin kafa sansaninsu a cikin dajin da ke yankin New Bussa a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Kwamishinan Kananan Hukumomi, Masarautu da Harkokin Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya ce, “An aika mayakan ISWAP da dama lahira, an kuma cafke wasu da dama da a halin yanzu suke tsare a hannun ’yan sanda.”
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata, kwamishinan ya ce ragargazar da sojoji suka yi wa ’yan kungiyar ta zama dole ne ganin yadda suke shigowa daga wasu jihohi suna neman yin kakagida a dajin.
A cewarsa, ’yan ta’adda na sha’awar zama a sassan Jihar Neja ne saboda yadda Allah Ya albarkaci jihar da yawan dabbobi da amfanin gona, amma gwamnatin jihar ta dauki matakan yin maganin su.
Ya ce, “Mun dauki kwararan matakai domin tabbatar da ganin ’yan bindiga da aka fatattako ba su koma wadannan yankunan ba.”