✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tseratar da mata da yara 30,000- Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan-Ali ya ce sojoji sun tseratar da akalla mata da kananan yara guda 30,000 daga hannun ‘yan Boko Haram. Ministan ya…

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan-Ali ya ce sojoji sun tseratar da akalla mata da kananan yara guda 30,000 daga hannun ‘yan Boko Haram.

Ministan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da mutane a yayin wani taron kara wa juna sani tsakanin sojoji da sauran jami’a tsaro a Maiduguri, inda ya ce lallai jami’an tsaron Najeriya sun samu nasara matuka a yakin na Boko Haram.

Sannan ya kara da cewa, “Zan yi amfani da wannan damar in sanar da ku cewa sojojinmu na kasa tare da hadin gwiwar abokanan aikinsu na sama sun yi wa Boko Haram mummunar ta’adi a farmakin da suka kai kwanan nan a cikin dajin Sambisa.”