✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin Sojoji Ya Yi Hatsari A Kaduna

Hatsarin ya auku ne a kusa da filin saukar jiragen sama na sojoji a garin Kaduna.

Wasu matuƙan jirgi biyu na rundunar sojin saman Najeriya (NAF) sun tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya rutsa da su yayin da dawowa daga atisayen da suka saba yi.

A cewar daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, hatsarin ya afku ne a kimanin tazarar mil 3.5 daga filin jirgin saman sojin da ke Kaduna.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:35 na ranar Alhamis a kusa da filin saukar jiragen sama na sojoji a garin Kaduna.

Sanarwar ta ce hukumomin sojin saman sun ba da umarnin gudanar da bincike na farko don gano musabbabin hatsarin jirgin.

Hatsarin dai ya biyo bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-35P na sojin saman Najeriya da ya faɗo a cikin watan Disamba, kuma shi ne karo na uku da ya afku tun watan Yuli.