A cikin mako guda, sojojin Najeriya sun sami nasarar halaka ’yan ta’addan ISWAP masu yawa lokacin da suka yi yunkurin kai wani hari a yankin Damboa da ke Jihar Borno.
Dakarun runduna ta 25 ta Operation Hadin Kai a yankin na Damboa ne suka yi wa ’yan ta’addan kofar rago sannan suka ragargaje su.
- 7 daga cikin kowane yaro 10 a Jigawa na rayuwa cikin kangin talauci – UNICEF
- Mutum 3,200 sun amfana da zakkar miliyan N10 a Kazaure
’Yan kungiyar ta ISWAP dai sun kaddamar da harin da bai samu nasara ba ’yan sa’o’i bayan sun yi mubayi’a ga sabon “Khalifan ISIS,” Abu al-Hussein al-Husseini al-Qurashi.
Bayanai sun nuna cewa ’yan ta’addar da ba a tantance adadinsu ba sun kai hari garin Wajiroko a cikin motoci kirar MRAP guda biyu da manyan motoci kirar Hilux guda shida dauke da bindigogin na harbo jiragen sama.
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa harin na ’yan ta’adda ya haifar da tada bama-bamai da dama da suka harba daga yankin Gubub na garin.
Dakarun masu sojin Najeriya dai sun tsaya tsayin daka inda suka yi artabu da ’yan ta’addan a wannan kazamin fadan da aka kwashe kusan mintuna 40 ana gwabzawa.
Daga karshe an tilastawa ’yan ta’addan tserewa daga wurin bayan sun samu asarar rayuka masu yawa.
’Yan ta’addan da suka tsere ba a san ko su waye ba, kuma tuni dakarun sojin Najeriya da ke Sabon Gari da Damboa karkashin jagorancin Birgediya Janar BO Omopariola, Kwamandan Brigade 25, suka yi musu kwanton bauna a hanyarsu ta tserewa inda suka yi raga-raga da su tare da lalata manyan motocinsu biyu dauke da mayaka da dama.
Kazalika, sojojin sun sami nasarar kwato bindiga samfurin x FN guda daya, da kirar AK-47 guda biyu bindigogi da na’urar harbo jirgi guda daya da bama-bamai da gurneti da kuma albarusai masu yawan gaske, daga hannun ’yan ta’addan.