Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta nesanta kanta da Kwamnado Jamila Abubakar, jami’ar da ta zargi sojojin kasar Chadi da sayar da makamansu idan suka shiga matsalar kudi.
Jamila dai ta yi zargin ne yayin taron jin ra’ayin jama’a da Kwamitin Tsaro na Majlisar Wakilai ya shirya a Abuja ranar Litinin.
- Yadda dauke wutar lantarki ya girgiza tattalin arzikin China
- ’Yan daba sun fille kan mutum sun buga kwallo da shi
Ta dai zargi yadda sojojin kasar ke sakin makamansu ba bisa ka’ida ba da cewa shi ne ummul-aba’isun kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.
Ta ce, “Ina daga cikin wadanda ke sahun gaba wajen yaki da Boko Haram, kuma zan iya bugun kirji in tabbatar muku da cewa wasu daga cikin kasashe makwabtanmu basu da makamai.
“Sam ba su da makamai. Yawancin makamansu tallafi ake basu daga…ba na son na ambaci suna…kasashen da suka ci gaba, a kokarinsu na tallafa mana suna kara ta’azzara matsalar tsaron Najeriya.
“Alal misali, za ka ga kusan duk sojan kasar Chadi yana da tsakanin makami 20 zuwa 30 a karkashin gadonsa. Idan ya shiga matsalar kudi, sai ya fito da su ya sayar tsakanin Dala 30 ko Dala 20. Ni nake fadin wannan gaba gadi, in akwai mai musu, ina kalubalantarsa,” inji ta.
To sai dai a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Suleiman Dahun, ya fitar ranar Talata, rundunar ta ce ba da yawaunta jami’ar ta furta kalaman ba.
“Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai a jiya [Litinin], 27 ga watan Satumban 2021 ya gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan kafa Hukumar Kula da Yaduwar Kananan Makamai. A yayi taron, wakiliyar Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta yi wasu kalamai, wadanda na kashin kanta ne, ba na rundunarmu ba, a kan yaduwar kananan makamai.
“Batun ya shafi alakarmu da makwabtan kasashe wadanda muke da kyakkyawar fahimta da su, kuma ra’ayin ya saba da na rundunarmu.
“Rundunarmu na nesanta kanta da ra’ayin wannan jami’ar. Muna jinjina wa gudunmawar da makwabtan kasashe suke bayarwa wajen yaki da yaduwar kanana da matsakaitan makamai,” inji sanarwar.