✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun musanta kashe fararen hula 10,000 a rikicin Boko Haram

Yaƙin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya mai sarƙaƙiya ne cike da ƙalubale.

Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta zargin da Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil-Adama ta Amnesty International, ta yi cewa fararen hula fiye 10,000 ne suka mutu a hannun dakarunta tun bayan ɓarkewa rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin ƙasar.

Aminiya ta ruwaito Shugaban Amnesty a Najeriya, Mallam Isa Sanusi yana zargin sojojin da hannu a mutuwar fararen hula da sauran nau’ikan cin zarafi, a wani jawabi da ya yi a tarin manema labarai a birnin Maiduguri a ranar Alhamis.

Mallam Sanusi ya ce tuni ƙungiyarsu ta shigar da ƙara gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC da ke birnin Hague kan zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam da take yi wa sojojin a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.

To sai dai yayin da take mayar da martani shalkwatar tsaron Najeriya (DHQ), cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana zarge-zargen a matsayin masu tayar da hankali, kuma marasa tushe ballantana makama.

“Duk da cewa yaƙin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya mai sarƙaƙiya ne cike da ƙalubale, muna bin ƙa’idojin da suka kamata.

“A duk lokacin da muka kama waɗanda ake zargi bayan ɗaukar bayanansu, mukan miƙa su hannun hukumomin da ya kamata domin a sake su ko a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Manjo Janar Edward Buba.

Manjo-Janar Buba ya kuma ce tuni sun gayyaci ƙungiyar ta Amesty zuwa ofishinta domin tabbatar da zarge-zargen.