Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kwato makamai da babura daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.
Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Laftanar-Kanar Musa Yahaya ne, ya sanar cewa hakan na daga cikin kokarin dakarun na kawar da ’yan bindiga daga dazukan Kaduna.
- Kisan Mauludi: Iyalan mutanen da aka kashe na neman diyyar N33bn daga Gwamnati
- NLC ta sa zare da gwamnati kan kin biyan ma’aikata N35,000 na Cire tallafi
Yahaya, ya ce sojojin suna aiki da sahihan bayanai a yankin Dogon Dawa zuwa Damari a Karamar Hukumar Igabi, inda suka yi wa maharan kwanton bauna a ranar Talata.
Ya bayyana cewa a yayin artabun, ’yan bindigar sun gudu sakamakon ruwan wutar da sojojin suka yi musu.
“Sojojin sun fatattake su, sun kuma kwato bindiga AK-47 guda daya da harsasai.
“Kazalika, sojojin da aka tura Kwanar Mutuwa a Birnin Gwari sun samu bayanan sirri kan ’yan bindiga.
“Dakarun sun yi saurin kai dauki yankin kuma nan take suka fatattake su,” in ji Yahaya.