Rundunar Operation Hadarin Daji ta Sojin Kasa ta ceto jarirai biyu da mata biyar a dajin Kuyambana da ke Jihar Zamfara, wadanda aka sace a ƙauyen Marange da ke ƙaramar hukumar Kagara a Jihar Neja tun a watan Janairun 2024.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Hadarin Daji, Laftanar Suleiman Omale ya fitar ranar Juma’a.
- Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 12 a Sambisa, Zamfara da Katsina
- Sojoji Sun Ceto Mutane 15 da aka sace a Zamfara
Omale ya ce, an kuɓutar da waɗanda lamarin ya rutsa da su ne ta hanyar farmakin da sojojin suka kai a yankin Kuyambana na Jihar Zamfara.
“An yi nasarar ceto mutanen ne sakamakon matsin lamba da sojojin suka yi wa ‘yan bindigar, wanda hakan ya sa aka kuɓutar da waɗanda abin ya shafa daga sansanin ‘yan bindigar.
“Samamen da sojojin suka yi a ranar 13 ga Maris, 2024 ya zama silar samun ‘yanci ta wadanda aka yi garkuwar da su,” in ji shi.