✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 12 a Sambisa, Zamfara da Katsina

Dakarun sojin sun hallaka 'yan ta'addar a samame daban-daban da suka kai.

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram 12 a dajin Sambisa da ke Jihar Borno, da kuma wasu mahara a Zamfara da Katsina.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Nwachukwu ya ce sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan a dajin Sambisa, inda suka kashe guda takwas a wani artabu da suka yi.

Ya ce a yayin farmakin, an yi kazamin artabu a tsakaninsu wanda ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda, sannan sauran suka tsere.

A cewarsa, sojojin sun kwato bindigogi guda biyar, babura biyu da kuma kayan abinci da dama daga hannun ‘yan ta’addan.

Nwachukwu ya ce a wani samame da sojoji suka kai Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina, sun kashe ’yan ta’adda biyu.

Kazalika, ya ce sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, harsashi guda 57 da kuma sauran makamai.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma ceto wani mutum, tare da kone baburan ’yan ta’addan guda biyu da kuma kone sansaninsu a karamar hukumar.

Ya ce sojojin sun kuma fatattaki ’yan ta’adda a kauyukan Dandalla, Madada, Dogon Karfe, Hayi, Gobirawan da Kango Kuyambana a kananan hukumomin Gusau da Maru a Jihar Zamfara.

A cewarsa, sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigogi kirar gida guda uku, harsasai, da kuma babur guda daya.

Har wa yau, Nwachukwu ya ce a ranar Lahadi sojojin sun kai samame tare da lalata masana’antar kera bindigogi ta IPOB da ke yankin Ekoli Edda da Amagwu Ohafia a Jihar Ebonyi da Jihar Abiya.

Kazalika, ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kai samame da hare-hare domin dakile ayyukan ’yan ta’adda a fadin Najeriya.