✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 10 a kusa da garin Buratai

Mayakan sun kai hari ne, amma sojoji suka dakile su

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile harin da kungiyar ISWAP ta kai a kauyen Kunnari kusa da garin Buratai a Karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno.

Rahoyon ya ce ’yan ta’addan sun mamaye garin ne da misalin karfe 3:00 na safe, Litinin 27 ga watan Maris, 2023 tare da yunkurin kai hari a sansanin sojoji.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa ’yan ta’addan na ISWAP sun zo ne a cikin manyan motoci da babura, inda suka yi ta harbe-harbe.

Sai dai majiyar ta ce cikin gaggawa sojojin suka mayar da martani da ya kai ga dakile wannan harin na su.

Majiyar ta kuma ce daga baya sojojin sun fatattaki ’yan ta’addan a wani artabu da suka yi da su tare da kashe takwas daga cikinsu nan take yayin da wasu kuma suka tsere daga wurin.

Sojojin sun ci gaba da fatattakar ’yan ta’addan ta hanyar tserewa inda suka tare wasu ’yan ta’addan guda biyu da suke kokarin gyara babur dinsu bayan ya tsaya tare da harbe su har lahira.

Sai dai majiyar ta ce wani soja daya ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga a artabun, inda nan take aka kai shi asibiti domin yi masa magani.