Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa ta CJTF sun kashe ’yan ta’addar Boko Haram takwas a dajin Sambisa na Jihar Borno.
An kashe ’yan ta’addan ne a ranar 20 ga watan Yuli, 2023, bayan da sojojin karkashin jagorancin kwamandansu na gaba suka lalata sansanoni uku a dajin.
- Wakar ‘cin zarafin Musulunci’: Matasa sun kone hotunan Davido a Borno
- Yadda Kanawa suka yi wa masu kudin Najeriya fintinkau a 2023
Wani kwararre a fagen yaki da ’yan tada kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana a Maiduguri cewa sojojin sun kai farmaki tare da fatattakar ’yan ta’addan a kauyukan Bula Daloye, Bulongu Dina da Mairamiri Dina.
A cewarsa, ’yan ta’addan tare da iyalansu sun yi ta kwana a gefen dajin tun shekarar 2015.
Wata majiyar soji a Maiduguri, ta kuma bayyana cewa bayan wani kazamin artabu da ’yan ta’addan, an kuma kwato makamansu da sauran kayayyaki, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga.
“Bayan an gwabza kusan tsawon awa daya da ’yan ta’addan, sojojinmu sun kuma ceto mata da kananan yara,” in ji majiyar.