✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Kanawa suka yi wa masu kudin Najeriya fintinkau a 2023

Dangote kadai ya mallaki dukiyar da ta zarce rabin kasafin kudin 2023 na kasar Najeriya mai yawan al'umma sama da miliyan 200

Kanawa biyu, Alhaji Aliko Dangote da kuma Abdulsamad Rabiu, sun zama ’yan Najeriya mafiya arziki a a shekarar 2023 da muke ciki.

Rahoton jerin attajiran duniya na 2023 da mujallar Forbes ta wallafa ya nuna Alhaji Aliko, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, ya mallaki Naira tiriliyan 11.2 (Dala biliyan 14.2), wanda ya zarce rabin kasafin kudin Najeriya na 2023 na tiriliyan 20.5.

Dukiyar Dangote ta zarce abin da mutum uku mafiya arziki a yankin Kudancin Najeriya suka mallaka — Cif Arthur Eze da Orji Uzo Kalu da kuma Cletus Ibeto.

Abdulsamad Rabiu, shugaban Rukunin Kamfanin BUA, mai samar da siminti da shinkafa da sukari da taliya shi ne a matsayi na biyu da Naira tiriliyan 6.3 (Dala biliyan 7.9), kimanin rabin abin da Dangote ya mallaka.

A watan Yuni ne Dangote mai masana’ntar siminti mafi girma a Afirka da ta kera motoci da kuma kamfanin kayan masarufi, ya kaddamar da matatar mai komai-da-ruwanka mafi girma a nahiyar.

Matatar, wadda za ta rika samar da tataccen mai da dangoginsa, ta lakume sama da Dala biliyan 9, kuma ana sa ran za ta wadatar da Najeriya a cikin gida, ta kuma biya bukatun wasu kasashen ketare akalla guda 12.

Na uku a jerin attajiran shi ne Mike Adenuga, Shugaban kamfanin Globacom, wanda dukiyarsa ta kai Naira tiriliyan 5 (Dala biliyan 6.3).

Arthur Eze mai kamfanin mai na Atlas Oranto Petroleum, shi ne na hudu da Naira tiriliyan 4.6 (Dala biliyan 5.8).

Na biyar shi ne Orji Uzo Kalu, mamallakin kamfanin SLOK Holding kuma Sanatan Abia ta Arewa, wanda dukiyarsa ta kai Naira tiriliyan 3 (Dala biliyan 3.8).

Cletus Ibeto, Shugaban Kamfanin Ibeto Group ne ya zo a matsayin na shin da Dala biliyan 3.2, wato kimanin Naira tiriliyan 2.5.
Mutum na 7 shi ne shugaban kamfanin The Chrome Group, Emeka Offor mai Dala biliyan 2.9, kimanin Naira tiriliyan
2.3.

Femi Otedole, mai kamfanin mai na Forte Oil ya mallaka Dala biliyan 2.7, kimanin Naira tiriliyan 2.1, a matsayi na takwas.

Sai dan siyasa, Sanatan Anambra ta Kudu, Andy Uba, a matsayi na tara da Dala biliyan 2.1 biliyan, kimanin tiriliyan 1.7.
Dan siyasa

Benedict Peters shugaban kamfanin Aiteo shi ne mutum na 10 a jerin attajiran Najeriya da dukiyar da ta kai Dala biliyan 2, kimanin tiriliyan N1.6.