✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji Sun Kashe ’Yan ISWAP A Kwalekwale A Tafkin Chadi

Dakaraun Operation Hadin Kai na Rundunar Sojan Saman Najeriya sun kashe wasu mayakan Kungiyar ISWAP da daman gaske a cikin kwalekwale a Karamar Hukumar Marte…

Dakaraun Operation Hadin Kai na Rundunar Sojan Saman Najeriya sun kashe wasu mayakan Kungiyar ISWAP da daman gaske a cikin kwalekwale a Karamar Hukumar Marte da ke Jihar Borno.

Sojojin sun yi wa ’yan ta’addan luguden wuta ne a ranar Asabar a kauyen kauyen Baranga da ke gabar Tafkin Chadi.

Majiyoyin leken asiri sun ce sojojin saman sun kai harin ne bayan samun rahoton cewa ’yan ta’addan suna dauke da makamai, inda suka shirin kai hari wasu yankunan gabar Tafkin Chadi.

Majiyar ta ce an kai harin ne tare da kashe dimbin ’yan ta’addan da ke cikin kwalekwale.

sojojin saman sun kuma lalata  wasu gine-ginen wadda aka Kone su kurmus da ke kusa da su wadda ake zaton  wasu ma’ajiyar kayan aikin su ne.

Majiyar ta Kara da cewa, ana ci gaba da kai farmakin ta sama a kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da nufin sai an ga bayan su.

%d bloggers like this: