Dakaraun Operation Hadin Kai na Rundunar Sojan Saman Najeriya sun kashe wasu mayakan Kungiyar ISWAP da daman gaske a cikin kwalekwale a Karamar Hukumar Marte da ke Jihar Borno.
Sojojin sun yi wa ’yan ta’addan luguden wuta ne a ranar Asabar a kauyen kauyen Baranga da ke gabar Tafkin Chadi.
Majiyoyin leken asiri sun ce sojojin saman sun kai harin ne bayan samun rahoton cewa ’yan ta’addan suna dauke da makamai, inda suka shirin kai hari wasu yankunan gabar Tafkin Chadi.
Majiyar ta ce an kai harin ne tare da kashe dimbin ’yan ta’addan da ke cikin kwalekwale.
- Direbobin Tankar Mai Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Kungiyar NUPENG
- Hukuncin Zaben Kano: Masu shirin zanga-zanga su shiga taitayinsu —’Yan sanda
sojojin saman sun kuma lalata wasu gine-ginen wadda aka Kone su kurmus da ke kusa da su wadda ake zaton wasu ma’ajiyar kayan aikin su ne.
Majiyar ta Kara da cewa, ana ci gaba da kai farmakin ta sama a kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da nufin sai an ga bayan su.