✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram da dama

Sojoji sun dakile harin ne a lokacin wani sintiri a tsakanin Kumshe da Banki

Wani Sabon tura da sojojin Operation Hadin Kai suka yi, ya kawar da mayakan Boko Haram da dama a wani harin kwanton bauna da suka yi musu.

A wani rahoto ya nuna cewa sojojin Birget na 21 masu sulke da ke Bama sun dakile harin ne a lokacin wani sintiri a tsakanin Kumshe da Banki.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama,kwararre kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata.

Majiyar ta ce ’yan ta’addar sun tayar da na’urar fashewar abubuwa sannan suka rika harbi babu kakkautawa, amma nan take sojojin suka fatattake su.

An ce dakarun na musamman sun dakile harin inda suka kashe maharan da dama ba tare da wani hasarar rayuka a bangaren sojojin ba.

An lalata motar Toyota hilux daya ta sojoji yayin da wasu sojojin suka samu raunuka a arangamar, kuma yanzu haka ana kula da su a hedikwatar rundunar da ke Bama a Jihar Borno.