Dakarun sashe na 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa (MNJTF) sun yi nasarar kashe ’yan ta’addan Boko Haram 23 a Jihar Borno.
Fafatawar ta faru ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, a kusa da Malam Fatori, bayan wata arangama inda sojoji suka dakile wani harin da maharan suka kai musu.
A cewar masanin harkokin tsaron nan a tafkin Chadi Zagazola Makama, sojojin sun yi wa mayakan na ISWAP kwanton bauna, inda suka yi ta harbe-harbe da ya yi sanadin mutuwar ’yan ta’adda 23 wasu da yawa kuma suka tsira da munanan raunuka.
A cewarsa, a yayin fafatawar wasu sojojin Najeriya biyu suka samu raunuka, amma ba a samu asarar rai ba a cikin sojojin.
- Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja
- PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu
Haka nan dakarun na MNJTF sun kwato makamai masu yawa daga hannun ’yan ta’addan da suka haɗa da bindiga kirar PKM, bindiga AK-47, gurneti da harsasai masu tarin yawa.