Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ’yan bindiga uku tare da kubutar da mutum 16 a wani samame da suka yi a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da wani bangare na Karamar Hukumar Igabi.
Aminiya ta tattaro cewa sojojin sun amsa kiran gaggawa da aka yi musu a kan hanyar Udawa zuwa Manini na hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna domin su dakile harin ’yan bindigar.
- Sabbin Kudi: ’Yan kasuwa za su rufe kasuwanni a Kebbi
- DAGA LARABA: Yadda matsin tattalin arziki ya sa wasu ’yan Najeriya suka rage cin abinci
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce bayan da suka dakile harin, sojojin sun kuma ceto wasu da suka samu raunuka sannan suka kai su asibiti don kula da su.
Ya ce sojojin sun kai daukin kauyen Gonan da ke Karamar Hukumar Igabi, inda suka yi kwanton bauna a kauyen Maraban Huda.
“Sojojin sun kama wasu ’yan bindiga sannan sun kashe wasu biyu. Sojojin sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kuma babura 10,” in ji shi.
Kaduna na daya daga cikin Jihohin Arewa da suka fi fuskantar hare-haren ’yan bindiga.