Jiragen yakin sojojin sama na Najeriya karkashin rundunar tsaro ta Operation Thunder Strike sun kashe ’yan bindiga kimanin 20 da ke kokarin sake kai hari makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna.
Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa an hangi gungun ’yan bindigar wadanda yawansu ya kai kimanin 50 a kan babura suna tunkarar makarantar.
- NDLEA ta kama miyagun kwayoyi na N2bn da aka shigo da su daga Indiya
- Yadda rikicin da ya kai Sadiya Haruna gidan yari ya samo asali
Idan za a iya tunawa, ko a watan Yunin 2021 sai da ’yan bindigar suka kai hari a makarantar sojojin.
A yayin wancan harin dai, ’yan bindigar sun sace wani soja mai mukamin Kyaftin, sannan suka kashe wasu guda biyu.
Sai dai a cewar majiyar tamu, sakamakon samun bayanan sirri kan yadda ’yan ta’addan ke kokarin sake kai hari makarantar ranar Alhamis, an tura jiragen yakin sojojin saman guda biyu, wadanda suka taso daga yankin Damari na Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar ta Kaduna.
“An hangi ’yan bindigar kusan su 50 a kan babura, wanda ganin jiragen ne ya sa suka fara guduwa zuwa cikin daji.
“Hakan yasa aka fara yi musu ruwan wuta ta sama, wadanda suke kokarin guduwa kuma suka hadu da dakaru a kasa.
“Kamar yadda yake bisa al’adar dakarun, alkaluman da muka tattara zuwa ranar Juma’a na nuni da cewa an hallaka akalla ’yan bindiga 20.
“Bugu da kari, yunkurinsu na kunyata sojojin Najeriya a idon duniya ta hanyar sake kai wa NDA hari bai yi nasara ba,” inji majiyar.