Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta ce sojoji sun sami nasarar kashe rikakkun ’yan bindiga hudu a wani tsauni da aka fi sani da ‘Maikwandaraso’ a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar.
An kashe ’yan bindigar ne bayan wata musayar wuta tsakaninsu da sojoji a yankin, a yunkurin da jami’an tsaro ke yi na fatattakarsu.
- An yi garkuwa da mutum 2 da suka je biyan kudin fansa a Bayelsa
- COVID-19: Saudiyya za ta biya iyalan ma’aikatan lafiyar da suka mutu N54m
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.
Ya ce wadanda aka kashe din suna hada da Alili Bandiro da Dayyabu Bala da Bala Nagwarjo da kuma Sulele Bala.
Sanarwar ta kara da cewa an kuma karkashe wasu da dama yayin wasu zafafan hare-haren da aka kai musu ta sama.
“Bayan samun rahoton wannan nasarar, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana farin cikinsa a kan haka tare da godewa sojojin bisa namijin kokarin da suke yi ba kakkautawa wajen kakkabe bata-gari,” inji Kwamishinan.
Maikwandaraso dai na dab da kauyen Karshi, kuma ya yi iyaka da dazukan Kawara da Malul, wadanda suka yi kaurin suna a yankin Karamar Hukumar ta Igabi, kuma nan ne aka yi ittifaki ya zama maboyar ’yan bindigar.