✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 26 a Borno

Dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) sun yi hallaka ’yan ta’addar Boko Haram da ISWAP 26 tare da dakile harinsu a yankin Tafkin…

Dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) sun yi hallaka ’yan ta’addar Boko Haram da ISWAP 26 tare da dakile harinsu a yankin Tafkin Chadi.

Masanin tsaron nan na Zagazola Makama ya ce ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba sun yi yunkurin kai hari a wani gidan man fetur a yankin Soudeye da ke kusa da Borgogorou a Jamhuriyar Nijar, a ranar Asabar, amma sojoji suka fatattake su bayan shafe sama da sa’a guda na musayar wuta da ya yi sanadin hallaka ’yan ta’addar.

Wata majiyar tsaro ta ce,  “Mun kirga gawarwaki 26, akwai yiwuwar karin wadansu saboda wasu gawarwakin sun bazu a ko’ina.

“Da farko sun zo da manyan bindigogi guda uku muka kashe su duka muka lalata motocin uku daga nan ’yan sintiri na ISR suka hango karin wasu biyu da suka gudu da dare kuma gama da su.”

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya a Tafkin Chadi, cewa sojoji sun fatattaki ’yan ta’addan, kafin hadakar rundunar sojojin sama ta MNJTF da ta kunshi Najeriya da Nijar ta kai hare-hare ta sama da dama.

Majiyar ta ce, jirgin sama na MNJTF ya bi sawun maharan da ke tserewa tare da lalata wasu karin bindigogi guda biyu inda suka kashe mutanen da ke cikinsa.

Majiyar ta kara da cewa dakarun gwamnatin ba su samu asarar rayuka ko jikkata ba.

Wata majiyar kuma ta shaida wa Zagazola cewa, Kwamandan Rundunar ta MNJTF ya yabawa rundunar saboda kokarin da suka yi, ya kuma umarce su da su tabbatar da halaka mayakan Boko Haram da ISWAP baki daya a yankin Tafkin Chadi.

An ruwaito Kwamandan Rundunar yana cewa “Muna da kwarin gwiwa kuma a shirye muke mu ci gaba da kashe su har sai sun mika wuya ba tare da wani sharadi ba a Tafkin Chadi.

“Mun yi imanin cewa ragowar su ne ke haifar da mafi yawan matsalolin da ke faruwa a cikin Najeriya amma sun samu kwarin gwiwa a nan (Nijar) kuma dole ne mu gama da su a nan wannan umarni ne daga shugabannin ma’aikatanmu kuma mu yi biyayya.”

Idan dai za a iya tunawa, rundunar leken asiri ta COIN ta tsananta kai hare-hare ta sama a maboyar mayakan Boko Haram da ISWAP a yankin Tafkin Chadi Tumbus na Abadam da Marte da ke karkashin Operation Desert da Lake Sanity ya sanya ’yan ta’addan neman mafaka a bakin kogi tsakanin Nijeriya da Jumhuriyar  Nijar a’ yan kwanakin nan.

Majiyar ta ce maboyar ’yan ta’addar sun hada da Lumburam da Fiyoo da Lada da Jarwaram, wadanda ke gabar kogi tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Ta bayyana cewa su ne aka yi amfani da su wajen tsara kai hare-hare a Gaidam da Kannama da Buni Yadi da sauran yankunan Arewa maso Gabas da a kwanan nan ke fuskantar yawaitar hare-hare.