✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP 10 A Borno 

An kashe mayakan ne bayan da sojojin kasa suka dakile wani hari

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) tare da Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa sun kashe ’yan ta’addan kungiyar ISWAP 10  a yankin Arege da ke Karamar Hukumar Abadam a Jihar Borno.

An kashe mayakan ne bayan da sojojin kasa suka dakile wani hari ta hanyar amfani da na’urar fashewar ta (VBIED) a ranar 10 ga Mayu, 2023.

Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya, a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana a Maiduguri cewa ’yan ta’addan sun yi wani gagarumin yunkuri na far wa sojojin kasa.

A cewarsa, ’yan ta’addan sun fuskanci turjiya mai tsanani, inda suka yi artabu na sama da sa’a guda.

Ya kara da cewa sojojin kasa tare da goyon bayan rundunar sojojin sama sun kashe ’yan ta’addar da dama, yayin da wasu kuma suka gudu da raunin harbin bindiga.

“Haka zalika sojojin sun lalata motocin ‘yan ta’addan biyu,” in ji shi.