Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da nasarar da dakarun kasar suka yi ta kashe wasu mutum biyu ‘yan tawagar shugaban masu ta da zaune tsaye a yankin Binuwai, Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana.
Rundunar ta kuma yi nasarar kama wata tawagar ’yan fashi a jihar Nasarawa.
Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro Manjo-Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ranar Lahadi a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Janar Enenche yana cewa an samu nasarar kashe ’yan fashin ne bayan tura rundunar sojoji a yankin Gbise da Zaki Biam da ke cikin jihar Binuwai.
Sannan aka sake tura wasu sojojin ayari hudu daga jihar Taraba, inda suka kai farmaki maboyar Gana da ke kauyen Mtan a gundumar Utenge ta Karamar Hukumar Katsina-Ala ranar Asabar.
Bayan kashe mukarraban Gana, sojojin sun raunata wasu da dama.
Ya kara da cewa sakamakon samamen da sojojin suka kai wa ’yan fashin an samu rahoton Gana ya tsere da raunukan harbin bindiga.
Makaman da aka kwato
Sojojin sun yi nasarar kwato makamai da suka hada da: Bindiga mai fitar da arsashi kirar gida, da wasu kananan bindigogi shida duk kirar gida da kuma wasu bindigogi da ake yi dura arsashi biyu da bindigar harbi ka ruga daya.
“Sauran abubuwan da aka samu akwai bindigogi pistol biyu, da pistol mai arsashe da yawa biyu da wasu makamai 27 da babura biyu da kayan sarki da Janerata daya da barkonon tsohuwa jaka daya da wasu layoyi.
An dai lalata wasu kayayyakin Gana da gidansa.
Samamen da aka kai Nasarawa
Daraktan yada labaran ya bayyana cewa, an tura rundunar sojojin yankin Ondori cikin Karamar Hukumar Doma a jihar Nasarawa inda suka kai samame a sansanin ’yan binidiga na Bassa da ke kauyen Kpelebewa a yankin Rukubim, sannan suka samu nasarar kame mutum bakwai.
Janar Enenche ya kara da cewa, sun samu rahoton ’yan bindigar na shirin kai hari a wata unguwar Tibi sakamakon rikicin fegi.