Sojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji, Albdulkarim Boss a kauyen Marina da ke Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne a sakamakon barin wutar da wani jirgin yaki da sojin suka yi a kan maboyar ’yan ta’addan a karshen mako.
- Wainar da aka toya a makon farko na Firimiyar Ingila ta bana
- ’Yan bindiga sun sace amarya da angonta a Katsina
Wata majiya ta shaida cewa, Abdulkarim Lawal wanda aka fi sani da Abdulkarim Boss ko Abdulkarim face-faca, an jima ana farautarsa kafin a hallaka shi a wannan lokaci.
Ko a jiya [Asabar] sai da mutanen garin ‘Yan Ukku suka hada mashi wasu kudi suka ba shi da zummar kyalesu su huta da hare-harensa su samu damar ci gaba da ayyuka a gonakinsu, lamarin da ya ce zai yi nazari a kai bayan ya karbe kudin,” a cewar majiyar.
Abdulkarim ne ya jagoranci muggan hare-haren ta’addanci da dama a yankunan arewacin Najeriya da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Bayanai sun ce Abdulkarim shi ne kasurgumin dan daban dajin da ya addabi yankunan Illela, Marina, Kukar Samu, ‘Yan Ukku da sauran yankunan Kananan Hukumomin Safana, Danmusa, Batsari da wasu yankuna na Jihar Zamfara
Abdulkarim ne ya jagoranci muggan hare-haren ta’addanci da dama a yankunan arewacin Najeriya da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Wasu rahotanni na cewa shi ya jagoranci harin da aka kai kan ayarin motocin Shugaban Kasa a Daura da kuma kashe wani babban jami’in dan sanda a yankin Dustinma a cikin watan Yuli.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Abdulkarim shi ne dan ta’addan da a tarihin munanan hare-haren da aka kai wa kauyen Marina, har yankan rago ya yi wa mutane a farkon mulkin Gwamna Aminu Bello Masari a 2015.
Sai dai har zuwa hada wannan rahoto, rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) bata ce komai ba a kan lamarin.
Kazalika, neman jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayarsa ba.